Latest comedy  |  Labarain Hausa  |  NEWS  |  NAIJA MUSIC VIDEO AUDIO  |  Labarain Wasanni|

« | »

Yadda coronavirus ta shiga fadar shugaban Najeriya Buhari

Posted by on March 25th, 2020Labarin da ya bayyana cewa shugaban ma’aikata a fadar shugaban Najeriya, Abba Kyari, ya kamu da coronavirus ya ja hankalin ‘yan kasar sosai saboda girman mukaminsa.

Majiyoyi a fadar shugaban Najeriya ta Aso Rock da ke Abuja da dama sun bayyana cewa sakamakon gwajin cutar da aka yi wa Malam Abba Kyari ya nuna cewa ya harbu da cutar numfashi ta coronavirus.

Duk da yake ya zuwa yanzu, hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasar ta sanar da mutum sama da 40 da suka kamu da cutar, amma Abba Kyari shi ne babban jami’in gwamnatin kasar da ya harbu da covid-19.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ambaci sunansa ba a tsarin ta na rashin ambatar sunan wadanda suka kamu tun da fari, sannan gwamnatin NAjeriya ba ta tabbatar ba a hukumance duk da tuntubar da BBC ta yi ta yi wa mutane daba-daban a fadar shugaban kasar.

Rahotanni na cewa shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasar ya kai ziyarar aiki kasar Jamus, ranar 7 ga watan Maris kuma ya koma Najeriya ranar 14 ga watan na Maris, ko da yake a lokacin bai nuna alamun rashin lafiya ba.

Sai dai masu sharhi na ganin ya kamata tun lokacin da ya koma Najeriya ya killace kansa domin yin biyayya ga umarnin da gwamnatin kasar ta yi cewa duk mutumin da ya koma kasar, to ya killace kansa tsawon mako biyu kafin ya soma gana wa da jama’a.

Hasalima, wasu rahotanni sun ce tun lokacin da ya koma gida, Abba Kyari ya halarci taruka daban-daban kan matakin da gwamnati take dauka domin shawo kan cutar ta COVID-19.

Ko da a makon jiya mai dakin shugaban kasar, Aisha Buhari, ta sanar da cewa ‘yarta ta killace kanta bayan komawarta Najeriya daga Birtaniya.

Ta ce ‘yar tata, wadda ba ta ambaci sunata ba, ta killace kan nata ne saboda shawarar da hukumomin lafiyar kasar suka bayar.

Tuni dai ‘yan kasar, ciki har da manyan ‘yan siyasa da jami’an gwamnati suka soma taya shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar alhini.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter Alhaji Atiku Abubakar, wanda shi ma dansa ya kamu da cutar, ya yi addu’ar samun sauki ga Abba Kyari.

“Ina yin addu’a ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari. Allah ya kare mu ga baki daya, kuma ya ba shi lafiya,” in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.

https://twitter.com/atiku/status/1242561532296417282?s=19

Wacce barazana hakan zai yi ga sauran jama’a?

Rahotanni sun ce tun bayar komawar Abba Kyari Najeriya, ya gana da manyan jami’an gwamnati da gwamnoni da ‘yan kasuwa da dama.

A makon jiya ne, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar ya jagoranci tawagar da ta je Lokoja, babban birnin jihar Kogi, domin mika sakon ta’aziyyar Shugaba Buhari ga Gwamna Yahaya Bello, wanda mahaifiyarsa ta rasu kwanakin baya.

Kazalika, wasu rahotanni sun ce Abba Kyari ya halarci wani daurin aure a karshen makon jiya a Abuja, babban birnin kasar, wanda manyan mutane irin su Aliko Dangote da Gwamna Aminu Bello Masari suka je, kuma sun zauna kurkusa da juna.

Yaya tsarin aikinsa yake?

A matsayinsa na shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Malam Abba Kyara yana da ruwa da tsaki a kan kusan komai da ya shafi shugaban kasar.

Shi ne mutumin da yake tsara komai game da ayyukan shugaban kasar, sannan yakan gana da akalla mutum 20 a kowacce rana, a cewar wasu ma’aikatan fadar ta shugaban Najeriya.

Wani dan jarida da ke dauko rahotanni a fadar shugaban Najeriya, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya shaida wa BBC cewa a kullum Abba Kyari yana gana wa da Shugaba Buhari akalla sau hudu.

Kazalika yana ganawa da gwamnoni da ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati wadanda ke son gana wa da shugaban kasa.

Rahotanni sun ce ganin irin mutanen da ke gana wa da abba Kyari a kullum, wasu daga cikinsu na fuskantar hadarin kamuwa da cutar, musamman wadanda suka yi musabaha ko kuma zama kurkusa da shi.

Tuni dai rahotanni suka ce da yawa daga ma’aikatan fadar shugaban kasar sun killace kansu.

Coronavirus ta yi ‘ajalin Suleiman Achimugu

Coronavirus: Mutum daya ya mutu a Najeriya

Abba Kyari ya kamu da cutar coronavirus – Reuters

Hamisu Breaker Official Video Nagane duniya

Hamisu Breaker Karnin Sako Official Music

Share this:

Like this:

Advertisements


RECOMMENDED SONGS FOR YOU

» Prince Mighty – Marry ( Prod By Chidony) » AUDIO+VIDEO: Pmartt – IG (Prod. By BDZ) » Peesmurls x Limerick x Chima – Feelings » VIDEO: Lil Dee Feat. Otega – Motivation (Remix) » Hamisu Breaker Official Video Nagane duniya » Sterlinboy ft Kastro – Mystical » MUSIC: Naidsin – Temilade » [Mp3] Mavel Tee – Aje (Wealth) » [Music] Elmuax -Ft- SukzyAfrica- Ft- Elzino – BABANEH (Prod. By Geezbeat) » Hamisu Breaker Official Audio Zuciya 2020
Checkout Lastest Hausa comedy Want Latest Hausa Audio? Click HereOR


CLICK TO DROP YOUR COMMENT

Share this post with your Friends on


No Responses Yet

Leave a Reply

Your Name (required)

Your Message:

NOTE:- After Dropping your comment, Wait for few minutes, your comments will appear after Moderation Bahaushiya care about !!
Go Back To The Top


Yadda coronavirus ta shiga fadar shugaban Najeriya Buhari


Coronavirus ta yi ‘ajalin Suleiman Achimugu


Coronavirus ta yi ‘ajalin Suleiman Achimugu

« | »