Latest comedy  |  Labarain Hausa  |  NEWS  |  NAIJA MUSIC VIDEO AUDIO  |  Labarain Wasanni|

« | »

An kama mata da miji da manyan bindigu a jihar Kebbi

Posted by on July 9th, 2020


TA’ADDANCI

An kama mata da miji da manyan bindigu a jihar Kebbi

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kebbi, ta cafke wani mutum da ake zargi dan daban daji ne dauke da man bindigu biyu kirar AK-47 a kwaryar Birnin Kebbi.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi, Agunbiade Oluyemi-Lasore, shi ne ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai cikin babban birnin jihar a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa, an cafke mutumin da ake zargi tare da matar sa a ranar 29 ga watan Yuni, yayin da wata tawagar ‘yan sanda ke gudanar da bincike a kan hanyar garin Birnin Yauri zuwa Zuru.

Sufeto Janar na ‘yan sanda; IGP Muhammad Adamu Hakkin mallakar hoto; Premium Times
“A ranar 29 ga Yuni, wata tawaga ‘yan sanda yayin da suke bakin aiki a kan titin Birnin Yauri zuwa Zuru, sun kama Umaru Usman, wani mutumin kauyen Zangon Labandi na karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

“An kuma kama shi tare da matarsa, Halima Adamu, dauke da manyan bindigogi biyu kirar AK 47 da kuma alburushai 154.”
“Haka zalika jami’an ‘yan sandan sun kamu ma’auratan da kakin sojoji da kuma layu a tattare da su.”

A yayin gudanar bincike, an kuma kama Taru Mai Unguwa, wani mutumin kauyen Danmaraya na karamar hukumar Ngaski ta jihar Kebbi , da ya ke tattaro wa ‘yan ta’adda bayanan sirri.

Mun gano aikin da APC ke son Ganduje ya yi mata a zaben jihar Edo – PDP

SADAUKIN GASKE LATEST INDIAN HAUSA 2020

Mu muka kashe Dr Okpara Enoch a Gusau Abubakar Namalika

Ta kuma faruwa Rikicin Kannywood Adam A Zango Da Bashir Mai Shadda

GIDAN BADAMASI SABON SHIRI ZANGO NA BIYU

Hamisu Breaker Official Video Juruma 2020

Share this:

Like this:

Advertisements


RECOMMENDED SONGS FOR YOU

» Ugobest Music Presents ‘Street Light’ Free Beat For All Artistes To Use » Download Video:- Reminisce Ft Fireboy – Ogaranya » UMAR BAKINKA OFFICIAL SONG 2020 » Mu shakata » [Music] GENJOW_Flexing » DONMATE – OJA » LATEST HAUSA SONG DAJIN SAMBISA VIDEO 4 » BALA USHER OFFICIAL AUDIO – NI NAKU NE » ZAMAN LAFIYA OFFICIAL AUDIO BY BALA USHER X ANASKO » DJ Flozy – Best Of Flavour Mixtape
Checkout Lastest Hausa comedy Want Latest Hausa Audio? Click HereOR


CLICK TO DROP YOUR COMMENT

Share this post with your Friends on


No Responses Yet

Leave a Reply

Your Name (required)

Your Message:

NOTE:- After Dropping your comment, Wait for few minutes, your comments will appear after Moderation Bahaushiya care about !!
Go Back To The Top


Makudan Kudade: Sanata Lawal Hassan


Nupe ndako kutigi latest Album Nna 2020


Nupe ndako kutigi latest Album Nna 2020

« | »