Latest comedy  |  Labarain Hausa  |  NEWS  |  NAIJA MUSIC VIDEO AUDIO  |  Labarain Wasanni|

« | »

Kutun ECOWAS ta umurci Gwamnatin Najeriya ta biya Sojojin da aka kora guda 244 hakkokinsu…….

Posted by on June 28th, 2020


Kutun ECOWAS ta umurci Gwamnatin Najeriya ta biya Sojojin da aka kora guda 244 hakkokinsu…….

Ahmed Abba

Kotun Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta umurci gwamnatin Najeriya da ta biya wasu sojojin kasar 244 da ta kora daga aiki a shekarar 2016 hakkokin su cikin gaggawa, bayan rundunar sojin kasar ta same su da laifin tserewa daga bakin daga a yakin da suke fafatawa da kungiyar Boko Haram.

A hukuncin da ta yanke, kotun ta hannu mai shari’a Keikura Bangura, tace korar sojojin daga bakin aiki ya saba ka’ida, saboda haka ta bukaci gwamnatin Najeriya ta biya su hakkokin su, duk da yake kotun taki amincewa da bukatar mayar da su bakin aiki da suka nemi tayi.

Kotun ECOWAS tace gabatar da korar sojojin daga aiki ba tare da gabatar su a gaban shari’a ba domin yi musu hukunci ya saba ka’ida, saboda haka ta bukaci gwamnati ta biya su kudaden su.

Alkalai 3 suka saurari karar suka kuma yanke hukunci, cikin su harda Gberi-Be Ouattara da ya jagoranci shari’ar da Dupe Atoki da kuma Keikura Bangura.

Ita dai rundunar sojin Najeriya tace ta dauki matakin korar sojojin ne saboda tserewa daga bakin daga lokacin da suke fafatawa da mayakan Boko Haram, yayin da sojojin ke cewa gwamnati bata basu cikakkun kayan aikin da zasu fuskanci mayakan ba.

Auren Wasa Na Shirin Zama Gaskiya

ANA KASHE BAYIN ALLAH TA KOINA A FADIN KASANNA DAN ALLAH BUHARI KA HAKURA KA KASA.DAMA MUN GAYAMUKU BAKU YARDABA YANZU GASHI KUNA GANI DA IDANKU.

Rahoton/RFI

Share this:

Like this:

Advertisements


RECOMMENDED SONGS FOR YOU

» Ugobest Music Presents ‘Street Light’ Free Beat For All Artistes To Use » Download Video:- Reminisce Ft Fireboy – Ogaranya » UMAR BAKINKA OFFICIAL SONG 2020 » Mu shakata » [Music] GENJOW_Flexing » DONMATE – OJA » LATEST HAUSA SONG DAJIN SAMBISA VIDEO 4 » BALA USHER OFFICIAL AUDIO – NI NAKU NE » ZAMAN LAFIYA OFFICIAL AUDIO BY BALA USHER X ANASKO » DJ Flozy – Best Of Flavour Mixtape
Checkout Lastest Hausa comedy Want Latest Hausa Audio? Click HereOR


CLICK TO DROP YOUR COMMENT

Share this post with your Friends on


No Responses Yet

Leave a Reply

Your Name (required)

Your Message:

NOTE:- After Dropping your comment, Wait for few minutes, your comments will appear after Moderation Bahaushiya care about !!
Go Back To The Top


Makudan Kudade: Sanata Lawal Hassan


Nupe ndako kutigi latest Album Nna 2020


Nupe ndako kutigi latest Album Nna 2020

« | »