Latest comedy  |  Labarain Hausa  |  NEWS  |  NAIJA MUSIC VIDEO AUDIO  |  Labarain Wasanni|

« | »

Coronavirus: Buhari ya tsawaita dokar hana fita a Abuja da Legas

Posted by on April 14th, 2020Shugaban Najeriya Muhammadu buhari ya tsawaita dokar hana fita na tsawon mako biyu a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja.

A jawabin da ya gabatar wa ‘yan Najeriya da aka watsa a kafar talbijin din kasar, shugaban ya ce shawarwari da rahoton kwamitinsa na yaki da Covid 19 da ya karba, sun nuna ya zama wajibi a tsawaita dokar.

Ya ce dokar za ta fara aiki daga 12:00 na daren Litinin.

Shugaban ya bayyana damuwa kan yadda masu kamuwa da cutar ke karuwa da kuma wadanda cutar ta kashe a sassan duniya da kuma Najeriya.

Ya ce sakamakon goyon baya da hadin kan da aka bayar, an samu nasarori da dama a tsawon mako biyu da aka hana fita.

Ya ce an aiwatar da matakan tabbatar da kiwon lafiyar jama’a, wadanda suka taimaka wajen gano wadanda suka kamu da cutar, da kuma killacewa da wadanda suka yi mu’amula da su.

Shugaban ya ce an gano kashi 92% na wadanda suka yi mu’amula da masu dauke da cutar. An kuma kara samar da wuraren gwaji da za a iya yin gwaji 1,500 a rana.

Ya kuma ce an yi wa ma’aikatar lafiya 7,000 horo kan yaki da cututtuka masu yaduwa, tare da tura tawagar hukumar NCDC a jihohi 19 na kasar.

Ya ce Abuja da Legas suna da cibiyoyin da za a iya kula da marar lafiya 1,000.

Coronavirus: Mece ce ita da kuma asalinta?
Coronavirus: BBC ta amsa tambayoyin da kuka aiko
Coronavirus a Najeriya: Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar
Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar, NCDC, ta ce mutum 323 aka tabbatar sun kamu da cutar.

Cutar ta kashe mutum 10 zuwa yanzu, 85 kuma sun warke.

Ranar 29 ga watan Maris ne karon farko da Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan kasar jawabi game da matakan da gwamnatinsa ke dauka a yaki da coronavirus.

Yadda coronavirus ta shiga fadar shugaban Najeriya Buhari

DABO DABO Adam A Zango Ft Ebadah (NT4)

BALA USHER FIA FIA VIDEO COVER Hausa version

Share this:

Like this:

Advertisements


RECOMMENDED SONGS FOR YOU

» UMAR BAKINKA OFFICIAL SONG 2020 » Mu shakata » [Music] GENJOW_Flexing » DONMATE – OJA » LATEST HAUSA SONG DAJIN SAMBISA VIDEO 4 » BALA USHER OFFICIAL AUDIO – NI NAKU NE » ZAMAN LAFIYA OFFICIAL AUDIO BY BALA USHER X ANASKO » DJ Flozy – Best Of Flavour Mixtape » [Music] Molex – Memories » Sterlinboy X Ktl – Champions
Checkout Lastest Hausa comedy Want Latest Hausa Audio? Click HereOR


CLICK TO DROP YOUR COMMENT

Share this post with your Friends on


No Responses Yet

Leave a Reply

Your Name (required)

Your Message:

NOTE:- After Dropping your comment, Wait for few minutes, your comments will appear after Moderation Bahaushiya care about !!
Go Back To The Top


ALHAMDULILLAH: An bude Masallacin Hajiya Sophia dake Turkiyya bayan da aka rufe


SADAUKIN GASKE LATEST INDIAN HAUSA 2020


SADAUKIN GASKE LATEST INDIAN HAUSA 2020

« | »